Sarkin Bauchi ya cika shekara 10 kan gadon mulki

Bauchi

Mai martaba Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu ya ce a tsawon shekarun da ya shafe a gadon mulki, an samu ci gaba ta fannin zamantakewar al’umma da samar da zaman lafiya.

Sarkin Bauchin na 11 ya bayyana wa BBC hakan yayin da ya cika shekara 10 da hawa kan karaga inda ya ce “mun daÉ—a samun ilimin rayuwa wajen tsoron Allah, wajen mu’amala da mutane,”

“wajen sanin shugabanci, wajen sanin zamantakewar al’umma, kuma mun daÉ—a samun ilimi wajen harka da gwamnati.”

A ranar Alhamis ne Sarkin ya cika shekara 10 a kan gadon sarauta, bayan ya gaji mahaifinsa Alhaji Sulaiman Adamu wanda ya rasu a 2010.

A cewarsa, zaman lafiyar da aka samu, abu ne daga Allah “mun san cewa wannan ba wai Æ™oÆ™arinmu ba, ba iyawarmu ba.”

Ya ce tun farkon hawansa kan mulki, sun zauna sun yi nazarin abin da ya kamata a yi domin samun maslaha kan matsalolin da ake fuskanta “mun zauna mun Æ™ari juna, na farko dai babbansu shi ne addu’a,”

“Allah shi ne mai iko a kan komai, muka sa addu’a a gaba muka ce abu ne da ya shafi kowa da kowa, da babba da yaro da mace da namiji, da mai sarauta da wanda ma bai da shi.”

“Ba ma wasa da duk wata shawara da aka kawo mana, abin da za mu iya yi sai mu yi, wanda muka ga na gaba ne sai mu sanar da gwamnati, kuma suna É—aukar matakai a kai.”

“Abin farinciki shi ne…..”

Sarkin na Bauchi ya ce kasancewar ranar da ya cika shekara 10 kan gadon mulki ta zo dai-dai da ranar da aka yi hawan Arfa, babban abin farinciki ne a garesa saboda “rana ce mai girma mai daraja mai albarka a wajen kowane musulmi a duniya.”

Sai dai Sarkin ya ce ba a gudanar da wasu shagulgula na bikin zagayowar wannan rana ba saboda annobar korona.

Ya ce rashin gudanar da biki ba abin damuwa bane ganin cewa annobar ta sa an dakatar da gudanar da wasu ibadu kamar Umrah da Tarawih da kuma tafsiri a masallatai.

“Abubuwan da muka yi addu’o kuma har gobe muna daÉ—a samun ‘yan uwa da abokan arziki suna taya mu da addu’oi.”

A Æ™arshe Sarkin ya ce addu’arsa kullum ita ce “Allah Ya raba mu da aikin da-na-sani.”

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...