Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya kai wa iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ziyarar ta’aziyar rayuwarsa.
Sarkin ya ziyarci iyalan marigayi Buhari ne a gidan tsohon shugaban kasar dake Kaduna.
A lokacin ziyarar mai martaba sarkin ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin ya kuma bawa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin da su ka yi


