Saraki na duba yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa

[ad_1]








Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki na duba yiwuwar yin takara da shugaban kasa Muhammad Buhari a zaben shekarar 2019.

Saraki wanda tun da fari ya nuna alamun neman zama shugaban kasa, ya fadawa jaridar Bloomberg cewa har yanzu yana cigaba da tattaunawa.

Duk acikin mako guda shugaban majalisar dattawan ya ziyarci tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Olusegun Obasanjo.

Saraki ya ce akwai buƙatar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP domin cika fatan da yake da shi na jagorancin kasarnan.

Makonni biyu da suka wuce ne shugaban majalisar dattawan ya sauya sheka daga jam’iyar APC ya zuwa PDP.

“Ina cigaba da tuntuba da kuma duba yiyuwar haka.Na yarda zan iya kawo sauyi,”aka jiyo shi yana fada.

“Jam’iyar PDP ta koyi darasi daga faduwar zabe da tayi a 2015 ina tunanin abin rashin dadi APC bata koyi wani darasi ba daga nasarar da tayi.”




[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...