Sanata Ned Nwoko ya fice daga jam’iyar PDP

Ned Nwoko sanata mai wakiltar mazaɓar arewacin jihar Delta ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyar PDP.

A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 30 ga  Janairu da aka turawa shugaban ƙaramar hukumar Aniocha North, Nwoko ya bayyana cewa ya fice ne daga jam’iyar PDP saboda rabuwar kai da kuma tsagi da aka samu a jam’iyar.

Sanatan ya ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyar ya shika alkawuran da ya ɗaukawa mutanen mazaɓarsa.

A kwanakin baya ne ake raɗe-raɗin cewa Nwoko ya shirya ficewa daga jam’iyar.

Jam’iyar adawa ta PDP ta shiga rikicin shugabanci inda a yan kwanakin nan mutane biyu suka ayyana kansu a matsayin masu yawa rike da muƙamin sakataren jam’iyar na kasa.

More from this stream

Recomended