Sanata John McCain na Amurka ya mutu

[ad_1]

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

John McCain: US war hero, maverick and political titan

John McCain, wanda tsohon sojan Amurka ne wanda daga baya ya zama sanata, ya kuma tsaya takarar shugabancin Amurka ya mutu yana da shekara 81.

Mista McCain ya mutu ne a jiya Asabar kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa ta bayyana.

Iyalan gidansa na tare da shi a lokacin da ya cika.

Likitoci sun gano cewa yana da wani tsiro a cikin kwakwalwarsa tun a watan Yulin 2017, kuma tun wancan lokacin yake karban magani.

Iyalansa sun bayyana cewa ya yanke shawarar daina shan maganin ne a ranar Jumma’a, kuma rabonsa da zuwa aiki a birnin Washington tun watan Disambar bara.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

John McCain ya tsaya takarar shugabancin Amurka tare da Sarah Palin (hagu) a 2008

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...