An bai wa tsohon dan kwallon Barcelona, Samuel Eto’o damar tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar Kamaru – Fecafoot.
‘Yan takara shida aka amince su tsaya takara cikin har da shugaban hukumar mai ci a yanzu Seidou Mbombo Njoya a zaben da zai gudana a ranar 11 ga watan Disamba.
Shi ma wani tsohon dan kwallon Kamaru, Jules Denis Onana an bashi damar shiga takarar amma kuma kwamitin tantancewa bai amince wa Emmanuel Maboang Kessack ya shiga takarar ba.
Sauran ‘yan takarar da za a fafata da su, sun hada da Crepin Soter Nyamsi, Justin Tagouh da kuma Zacharie Wandja.
Eto’o, mai shekaru 40, a cikin watan Satumba ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar a Kamaru duk da cewa an tayar da jijiyar wuya saboda yana da shaida zama dan wata kasar ban da Kamaru.
Eto’o, wanda ya murza leda a Inter Milan da Chelsea, ya samu takardar shaida zama dan kasar Spaniya ne lokacin da yake buga kwallo a Barcelona.