Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan hanyar Kano zuwa Hadejia.

Shiisu Adamu mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ya ce gobarar ta kuma yi sanadiyar jikkata wasu mutane sama da 50.

Adam ya ce yawancin mutanen da abun ya shafa na ƙoƙarin kwasar man fetur ne da ya malala daga cikin motar sanadiyar faɗuwar da tayi kafin daga bisani ta kama da wuta.

“Da misalin ƙarfe 11:30 na dare ranar Talata a garin Majia dake ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa wata motar tanka ta ƙwace daga hannun direbanta a kusa da Jami’ar Khadijah dake Majia inda ta kama da wuta,” ya ce.

“Direban ya baro Kano akan hanyarsa ta zuwa garin Nguru dake jihar Yobe lokacin da hatsarin ya faru,”

“Mun damu sosai duk da ƙoƙarin  jami’an ƴan sanda na gargaɗin mutane su kauce daga wurin hatsarin da ya shafi tankar mai amma  suka ƙi ji.”

“Mutane sun taru a wurin da hatsarin ya faru  hakan ne ya sa aka samu asarar rayuka da yawa,”

Ya ƙara da cewa an gudanar da jana’izar mutanen a ranar Laraba da safe a yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata ya zuwa asibiti garin Ringim.

More from this stream

Recomended