Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka rubuta jarabawar suka samu kiredit biyar zuwa sama a harshen Ingilishi da lissafi.

Shugaban NECO Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar NECO a ranar Alhamis da ta gabata a garin Minna na jihar Neja.

Farfesa Wushishi ya bayyana cewa mutane 1,376,423 da suka kunshi maza 706,950 da mata 669,473 ne suka yi rijistar jarabawar.

Shugaban na NECO ya yi karin haske kan sakamakon: “Yawan wadanda suka zana jarrabawar sun kai 1,367,736, wadanda suka kunshi maza 702,112 da mata 665,624. 

“Yawancin wadanda suka sami maki biyar da sama da haka, ciki har da Ingilishi da Lissafi, sun kai 828,284, wanda ke wakiltar kashi 60.55%.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...