Sakamakon gwajin da aka yiwa lokitocin China da suka zo Najeriya ya fito – AREWA News

A wani rahoto da majiyarmu ta wallafa, an bayyana cewa tawagar kwarrarun ma’aikatan Lafiya 15 da suka zo Najeriya daga China domin taimakawa kasar wurin yaki da COVID-19 basa dauke da kwayar cutar.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ne ya fadi hakan yayin taron da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da COVID-19 ya gudanar ranar Talata.

Enahire ya ce sakamakon gwajin da aka yi ya nuna dukkan yan kasar na China ba su dauke da kwayar cutar.

Wannan na zuwa ne bayan sun kwashe kwanaki 14 a killace domin tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

More from this stream

Recomended