Sadiya Faruq Ta Bayyana EFCC Kan Zargin Almundahanar Biliyan 37

Sadiya Umar tsohuwar ministan ma’aikatar jin kai ta amsa gayyatar da hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta yi mata.

Hukumar yaki da cin hancin na gudanar da bincike ne kan ma’aikatar da ta jagoranta a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari kan zargin almundahanar naira biliyan 37.

Sadiya ta rike mukamin ministan daga shekarar 2019 zuwa 2023.

A ranar 4 ga watan Janairu ne hukumar ta EFCC ta nemi tsohuwar ministar da ta kai kanta ofishin hukumar ba tare da ɓata lokaci biyo bayan rahotannin dake cewa taki girmama gayyatar da EFCC tayi mata.

A martanin da ta mayar tsohuwar ministar ta ce rashin lafiya ce ta hana ta amsa gayyatar.

A yayin da ta bayyana a ofishin EFCC a ranar Litinin, Sadiya Faruq ta ce tana alfahari da cewa ta hidimtawa Najeriya a matsayin minista kuma a shirye take ta kare duk wasu ayyuka da tayi lokacin da take kan mulki.

More from this stream

Recomended