Sadio Mane zai iya komawa Real Madrid, Barcelona za ta dawo da Neymar

Sadio Mane

Hakkin mallakar hoto
@10SadioMane

Dan wasan Liverpool Sadio Mane zai iya komawa Real Madrid, a cewar dan wasan Senegal Keita Balde, wanda ya kara da cewa zai yi wahala Mane, mai shekara 28, ya ci gaba da zama a Anfield “har abada”. (AS, in Spanish)

Barcelona za ta sake taya dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, domin ta dawo da shi daga Paris St-Germain. A shirye kungiyar take ta bayar da ‘yan wasan Faransa uku Samuel Umtiti, Ousmane Dembele da kuma Jean-Clair Todibo a matsayin yarjejeniya don karbo shi a daidai lokacin da suke fama da karancin kudi saboda annobar coronavirus. (Mundo Deportivo, in Spanish)

Ana sa ran dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, ya sabunta kwangilarsa a Manchester United kuma ana kallonsa a matsayin shugaba a kungiyar, a cewar dan jaridar Spaniya mai bayar da rahoto kan wasan kwallon kafa Guillem Balague. (Express)

Shahararren gola Gianluigi Buffon, mai shekara 42, ya amince ya tsawaita zamansa a Juventus. Hakan zai kasance karo na 19 da dan kasar ta Italiya ya ke sabunta kwantaraginsa a Turin. (Tuttosport, in Italian)

A shirye Fiorentina take ta sayar da dan wasan da Manchester United take son dauka Federico Chiesa, sai dai ta ce dan wasan na Italiya mai shekara 22 ba ya son barin kungiyar. (Sun)

Borussia Dortmund ta so karbo Mason Greenwood, mai shekara 18, daga Manchester United lokacin da United ta nemi dauko dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (ESPN)

Mai yiwuwa Arsenal ba za ta samu damar dauko Layvin Kurzawa daga Paris St-Germain ba. Dan wasan bayan na Faransa, mai shekara, 27, ya shirya tsaf don komawa PSG a karshen kakar wasa ta bana amma watakila yanzu a tsawaita kwangilarsa. (Sport)

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya tuntubi matar dan wasan Paris St-Germain Mauro Icardi da wakilinsa, Wanda Nara, a game da yiwuwar sayo dan wasan na Argentina. Icardi, mai shekara 27, a halin yanzu yana Inter Milan a matsayin aro daga PSG. (Tuttosport, in Italian)

A gefe guda, tsohon dan wasan Chelsea Diego Costa, mai shekara 31, zai iya barin Atletico a karshen kakar wasa ta bana. (Marca)

Arsenal, Chelsea da kuma Everton dukkansu suna yunkurin dauko dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel, mai shekara 22. (ESPN)

Inter Milan tana son sayo dan wasan Manchester United da Faransa Anthony Martial, mai shekara 24, idan basu dauko dan wasan da Barcelona take zawarci ba Lautaro Martinez a bazarar nan. (Gazetto Dello Sport, in Italian)

Sai dai kuma Barcelona ta shirya tsaf don rasa ‘yan wasanta da dama a bazara saboda annobar coronavirus. (ESPN)

More from this stream

Recomended