Sabon Kakakin Rundunar Tsaron Najeriya Ya Kama Aiki—VOA

0
ABUJA, NIGERIA – Cikin wani ‘dan kwarya-kwaryar bikin amsar ragama da ya wakana a babban ‘dakin taro na hedikwatar rundunar tsaron kasar, sabon daraktan labarun mayakan kasar, Janaral Gusau wanda ya yaba wa wanda ya gada, ya nemi ‘yan jaridu da kafafen yada labaru su ba shi hadin kai da cikakken goyon baya da bayyana wa duniya gaskiyar halin da tsaron kasar ke ciki.

Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki
Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki

Janaral Tukur Gusau yayi kiran samun kyakkyawar alaka tsakanin ‘yan jaridu da sojoji, yana mai cewa Alkalami ya fi takobi kaifi, inda yayi bayanin cewa tasirin kafafen yada labaru ka iya taimakawa wajen samar da mafita game da matsalar tsaro a kasar

Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki
Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki

Sabon kakakin Rundunar tsaron Najeriyar din ya ce yanzu da Najeriya ke dab da shiga yanayin hada hadar zabe a watan gobe na Fabrairu, ya roki manema labarai da su guji yada rahotannin da ka iya dakushe wa dakaru gwiwa da kuma ka iya taba mutuncin mayakan da a halin yanzu ke shirye-shiryen bai wa sauran hukumomin tsaro gudunmowa, a yunkurin samar da yanayin yin zaben cikin lumana da adalci.

Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki
Sabon Kakakin Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya Ya Amshi Ragamar Mulki

TARIHIN JANAR TUKUR GUSAU:

An haifi sabon kakakin hedikwatar rundunar tsaron Najeriyar a garin Gusau hedkwatar jihar Zamfara ran tara ga watan Janairun shekarar 1969, ya kuma shiga aikin soja a shekarar 1993, inda aka tura shi Sashen hulda da jama’a.

Janar Gusau wanda keda Digiri uku, ya samu digirin farko a kan kimiyyar siyasa daga Jami’ar Usmanu Danfodio dake Sokoto, sai digiri na biyu daga Jami’ar Ahmadu Bello dake zaria a fannin alakar kasa da kasa kana sai digiri na uku a fannin gudanarwa daga jami’ar Leicester da ke kasar Birtaniya kana ya kuma sami shaidar Diploma daga Cibiyar Hulda da Jama’a ta Kasa da ke Kaduna.

Sabon kakakin sojojin ya halarci kwasa kwasai a ciki da wajen Najeriya a kasasashen Afirka, Turai da Amurka irinsu Ghana, Burtaniya da Amurka.

Yayi aiki a rundunonin sojin kasar a sassa daban daban na Najeriya, ya koyar a makarantar horas da hafsoshin Najeriya wato NDA dake kaduna, bugu da kari ya kuma yi aiki a Brigade din sojojin Artillary na 33 dake Bauchi, da Brigade na 34 dake Owerri, da rundunar dakarun sa ido na majalisar dinkin duniya a kasar Laberiya, kana yayi aki a rundunar dake tsaron fadar shugaban kasa wao GUARDS BRIGADE, Sannan ya yi Mataimakin Kwamandan Makarantar horas da jami’an hulda da jama’a na rundunar sojojin Najeriya NASPRI.

Janar Tukur Gusau shine kakani rundunar yaki da Boko Haram na farko wato OPERATION LAFIYA DOLE, kana yayi kakakin ministan tsaron Najeriya, kana ya halarci cibiyar nazarin muhimman bukatun kasa ta NATIONAL INSTITUTE, dake Kuru a Jos, Jihar Filato inda yake shima mamba ne wato MNI., yana kuma da lambobin yabo irin su MSS, FSS, DSS, NSJ, OPZLM, RNM, FNARS da kuma lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNMIL.