Sabbin manufofin Najeriya 9 kan kasashen waje

Hakkin mallakar hoto
PHILL MAGAKOE

Image caption

Shuagaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaba kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa

Gwamnatin Najeriya ta sanarwa da jakadun kasashen da ke kasar sabbin manufofi tara da gwamnatin Muhammadu Buhari zata mai da hankali kansu nan da shekaru uku masu zuwa.

Mininstan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geoffery Onyeama ya shaida hakan yayin wata ganawa da kasashen duniya a babban birnin kasar, Abuja.

Ya ce ya kamata Najeriya ta nuna zahirin abun da tsare-tsaren ya kunsa sannan Najeriya za ta mai da hankali kan bukatar da ke akwai ta bai wa kasar fifiko fiye da komai.

Mista Onyeama ya zayyana manufofi guda tara kamar haka:

  • Samar da ingantaccen tattalin arziki mai dorewa
  • Bunkasa harkar noma domin samar da isasshen abinci da har za a fitar kasashen waje.
  • Samar da isasshen makamashi da wutar lantarki da kuma mai da dangoginsa.
  • Fadada harka sufuri da sauran ayyukan ci gaba.
  • Fadada kasuwanci ta yadda zai bunkasa da sana’o’in dogaro da kai da masana’antu.
  • Samar da hanyoyin janyo duk dan kasa a jika domin damawa da su cikin harkokin kasa da manufar rage talauci.
  • Fadada damar samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya cikin sauki da kuma inganta ayyukan ‘yan Najeriya.
  • Tsare-tsaren yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta harkar gudanar da gwamnati da samar da shigar kowa cikin harkar gwamnati ta yadda za a dama dasu.
  • Inganta sha’anin tsaro

Ministan ya kara da cewa gwamnatin Najeriya za ta bai wa kasashen hadin kai domin tabbatar da an cimma manyan manufofin tara na Najeriyar.

Ya kuma bayyana cewa duk da cewar Najeriya za ta mai da hankali sosai wajen gina tattalin arazikin kasar domin al’ummarta ta amfana, za kuma ta dukufa wajen yin aiki da ci gaba da kyakkyawar mu’amala da kasashe irinsu Nijar da Tchadi da Benin da kuma Kamaru da manufar hada kai da su ka yi wajen yaki da Boko haram.

A mataki na yanki kuwa, Onyeama ya ce, Najeriya za ta ci gaba da bayar da hadin kan yanki da kuma dangane da batun samar da kudi na bai daya na yankin.

Ministan ya ce, cinikayyar tattalin arziki a diflomasiyya shi ne ginshikin tsarin harkokin kasashen wajen Najeriya kuma gwamnatin za ta ci gaba da tallata cinikayyar yankin da na kasashen ketare da ke nahiyar.

Tun samun ‘yancin kan Najeriya a shekarar 1960, tsarin harkokin kasashen wajen Najeriya ya mai da hankali ne kan hadin kan nahiyar Afirka shi yasa ma ake kiran ta da babbar yaya a Afirka.

Mai da hankali da Najeriya ta yi wajen ci gaban Afirka ne ya taimaka aka samar da Tarayyar Afirka da ke sanya ido kan harkokin kasashen nahiyar.

Sai dai da wannan dan canjin da aka samu kan harkokin kasashen waje, wasu masana kan harkar na ganin cewa Najeriya za ta iya magance dukkan matsalolinta na cikin gida.

Mininstan ya kuma yi amfani da damar ganawar tasa da kasashen wajen inda ya yi musu gargadi cewa ka da su tafi kai tsaye zuwa fadar shugaban kasa ba tare da sun bi ta ma’aikatarsa ba.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...