Roma ta raba gari da kocinta Di Frrancesco

Roma

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Roma, Eusebio Di Francesco ya bar aikinsa nan take.

Di Francesco ya koma Roma da aiki a watan Yunin 2017, inda ya maye gurbin Luciano Spalleti.

Kocin ya kai kungiyar wasan daf da karshe a gasar kofin Zakaraun Turai ta Champions League ya kuma doke Barcelona a wasan kungiyoyi takwas, sannan ya yi na uku a teburin Seria A a shekarar farko.

Sai dai kuma Di Francesco ya shiga matsi bayan da Lazio ta doke Roma 3-0 a makon jiya da rashin nasara da ta yi a gidan Porto da ta kai aka fitar da su a gasar Champions League ta bana.

Watakila Claudio Ranieri wanda Fulham ta sallama a makon jiya ya karbi aikin horar da Roma wadda ya taba aiki da ita tsakanin 2009 zuwa 2011.

Roma tana ta biyar a kan teburin Seria A da tazarar maki uku tsakaninta da ta hudu Inter Milan.

More News

Matatar mai ta fatakwal za ta iya fara aiki a ƙarshen watan Yuni

Matatar mai ta Fatakwal mai tace mai ganga 210,000 a kowacce rana na iya fara aiki a karshen watan Yuli bayan dogon lokaci. Jami’in hulda...

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

ÆŠan takarar shugaban Æ™asa  a zaÉ“en 2023 Æ™arÆ™ashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...