
Rukuni na biyu na ɗaliban Najeriya da ke gujewa rikicin Sudan sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Hukumar NIDCOM dake kula da yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta ce yan Najeriya 130 da suka haɗa da mata 128 da kuma maza biyu sun taso daga filin jirgin saman garin Port Sudan a cikin jirgin kamfanin Tarco Airline inda suka sauka a filin jirgen saman Abuja da misalin karfe 03:15 na yamma.
Ana kuma saka ran jirgin kamfanin Azman da yanzu haka yake kasar Masar zai kwaso karin wasu yan Najeriyar zuwa gida.