Rikicin Sudan: Max Air Zai Kwaso Yan Najeriya 560 Daga Masar

Kamfanin jiragen sama na Max Air zai kwaso karin wasu yan Najeriya da rikicin Sudan ya rutsa da su.

Kamfanin ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa kamfanin zai yi amfani da jirgin sa kirar Boeing 747-400 domin kaso yan Najeriya 560 da yanzu haka suke makale a Masar bayan tserewa rikicin na Sudan.

Kawo yanzu dai dubban yan Najeriya ne suke can kan iyakar Sudan da Masar inda suke jiran a kwaso su zuwa gida.

A jiya ne dai rukunin farko na yan Najeriya da aka kwaso suka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja

More from this stream

Recomended