Mutane da dama sun jikkata, yayin da gidaje suka kone a sakamakon tashin hankalin da ya barke a garin Shimankar da ke Karamar Hukumar Shendam a Jihar Plateau a ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya dauki sa’o’i da dama, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali.
Wani ganau ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin wasu kungiyoyin gargajiya da wasu Musulmi game da gudanar da wasu al’adun gargajiya a yankin.
Tsohon dan takarar Sanata a shiyyar Plateau ta Kudu, Mista Tobias Kwanmen, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce rikicin ya rikide zuwa kone-kone na gidaje da kasuwanni.
Ya ce, “Tun da fari dai, rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin wasu masu bautar gargajiya da wasu Musulmi a yankin. An ce masu bautar gargajiya sun yi kokarin gudanar da bukukuwan su, amma wasu Musulmi suka hana su, wanda hakan ya haifar da cece-kuce da kuma rikici.”
Ya kara da cewa har yanzu ana tantance irin barnar da aka yi, yayin da jami’an tsaro suka hanzarta zuwa wajen domin shawo kan lamarin.
Gwamnatin Jihar Plateau ta tabbatar da afkuwar rikicin, tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Kwamishinar Watsa Labarai da Sadarwa ta Jihar, Joyce Ramnap, ta fitar da wata sanarwa, inda ta nuna matukar damuwa kan tabarbarewar zaman lafiya a yankin, tana mai yin kira da a zauna lafiya.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Rikici Ya Barke a Wani Yanki na Plateau Yayin Da Mutane da Dama Suka Jikkata
