Rikici da annoba sun sa miliyoyin mutane kauracewa gidajensu a 2019 | BBC news

People from the Nigerian town of Malam Fatori an its area, close to the borders with Niger and Chad, pass by a car with Chadian Gendarmes (in uniform) as they flee Islamist Boko Haram attacks to take shelter in the Niger's town of Bosso secure by Niger and Chad armies, on May 25, 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani sabon rahoton cibiyar kasa da kasa da ke sa ido kan mutanen da rikici ya dai-daita IDMC, ya ce sama da mutum miliyan 10 ne suka rasa matsugunansu tsakanin watan Janairu da Yunin bana.

Cikin adadin, mutum miliyan 3.8 ne suka bar gidajensu sanadiyyar yaki a sassan Nahiyar Afirka da kuma Gabas Ta Tsakiya, kuma akasarin rikicin ya faru ne sakamakon rashin bin ka’idojin yarjejeniyoyin zaman lafiya da bukatar tsagaita wuta da aka cimma a Syria da Yemen da Afghanistan da kuma Libya.

Rahoton wanda IDMC ya fitar ranar Alhamis ya ce babban birnin Libiya Tripoli, ya tsinci kansa cikin matsanancin rikici tun bayan barkewar yakin basasa a Libya.

Haka abin yake a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Habasha da kuma Najeriya wadanda su ma jerin hare-hare ya raba dubban jama’a da ga muhallansu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Munanan hare-hare a arewa maso yammacin Najeriya da kuma rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin tsakiyar kasar ya sa wasu karin mutanen neman mafaka fiye da adadin mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Rikici tsakanin al’umomi daban-daban da hare-haren ‘yan-ta-da-kayar-baya ya sa ke rura wutar rikici a tsakanin al’umomi a sassan Yammacin Afirka abin da ya ta’azzara yawan mutanen da suka bar gidajensu fi ye da yadda yankin ya gani a baya.

“Wannan adadi ya karu ne matuka, musamman yadda mu ke tunkarar karshen shekara,” a cewar rahoton.

Adadin ya nuna ba a daukar matakan dakile abubuwan da ke haddasa rikicin da rashin daidaiton da ake samu sannan al’amarin na janyo nau’ukan rikici kamar yadda Daraktan Cibiyar ta IDMC, Alexandra Bilak ya bayyana.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Annoba da dama ta sa wasu mutane miliyan bakwai rasa muhallansu.

Mahaukaciyar guguwa hade da ambaliyar ruwa ne ke janyo wannan abu da ke faruwa, sanadiyyar rashin kyawun yanayi da da yake sa yi wa annobar kallon zama ruwan dare.

Guguwar Fani ita ma ta jefa miliyoyin mutane cikin halin ni ‘yasu a Indiya da Bangladesh yayin da guguwar Idai ta afkawa Mozambique da Malawi da Zimbabwe da kuma Madagascar inda anan ma gwamman mutane su ka rasa muhallansu.

Ambaliyar ruwan ta yi mummunar barna a Iran inda annobar ta sha fi kaso 90 cikin al’ummar Ethiopia da Philippines da Bolivia.

La’akari da rahotannin da suka gabata da ke alakanta akasarin annobar da ta shafi yanayi ce ta afkawa yankunan a tsukin Janairu zuwa Yunin shekarar bara, Cibiyar ta IDMC ta kiyasta cewa yawan mutanen da suka rasa gidajensu zai rubanya a karshen shekararnan zuwa kusa miliyan 22.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Guguwar Fani ita ma ta jefa miliyoyin mutane cikin halin ni ‘yasu a Indiya da Bangladesh

Ba makawa wannan zai ayyana wannan shekarar a matsayin wadda ta fi samun mutanen da suka rasa gidajensu ta wannan yanayi.

”Bai dace Kasashen waje su ci gaba da yin burus da yankunan da dubun dubatar jama’ar da suka rasa gidajnesu ba. In ji Bilak.

“Dole mu tallafawa gwamnatocin kasashen da wannan ibtila’in kan shafa a kokarinsu na kare ‘yan gudun hijira da tabatar da zaman lafiya da kuma janyo kudaden shiga domin samar da ci gaba mai dorewa da iya rayuwa sakamakon sauyin yanayi.

“Idan aka yi haka ne za a iya rage halin na ni ‘yasu da tashin hankalin da miliyoyin mutane ke shiga sannan a kawo babban sauyi kan wannan adadi da aka bayyana a rahoton.”

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...