
Dan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmad ya yi kira da a kwantar da hankali tare da kaucewa rikici a jihar Lagos.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan an ayyana ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyar LP, Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa a jihar.
Tuni rahotanni suka nuna cewa wasu mutane sun rika kai hare-hare kan kasuwanni da wasu mutane da ba yan asalin jihar suke zaune ba.