Real Madrid: Wasa 15 a jere ba a doke ta ba a La Liga tun bayan cutar korona

Real Madrid

A wannan lokacin gasar kasashen duniya na hutu bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta amince a buga gasa ko wasannin sada zumunta tsakanin tawagogin kwallon kafa a fadin duniya.

Hakan ne ya sa zamu yi duba na tsanaki kan kwazon Real Madrid wacce ba ta sayi dan kwallo ko daya ba a bana duk da cinikayyar da aka gudanar, inda aka rufe kasuwa saye da sayar da ‘yan kwallo ranar 5 ga watan Oktoba.

Tuni dai Real Madrid ta yi wasa 15 a jere a gasar La Liga ba a doke ta ba, tun daga bayan jinyar cutar korona, kuma kawo yanzu ta ci wasa 13 da canjaras biyu jumulla.

Tun bayan da Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gidan Real Betis ranar 8 ga watan Maris 2020, sai da kungiyar ta lashe wasa 10 a jere a La Liga daga lokacin.

Kuma a wasan na 10 a jere ta lashe kofin La Liga na bara, bayan da ta doke Villareal 2-1 ranar 16 ga watan Yuli ta kuma lashe kofin gasar na 34 jumulla.

Sannan ta buga canjaras a wasan karshe a kakar da aka karkare ta bara a gidan Leganes da ci 2-2.

Kakar bana kuwa ta 2020-21, Real ta fara da canjaras a gidan Sociedad, sai kuma ta lashe dukkan karawa uku da ta yi wato da Betis da Valladolid da kuma Levante..

Cikin wasan La Liga 15 a jere da ba a doke Real ba, masu tsaron bayanta sun taka rawar gani, inda mai tsaron raga Thibaut Coutois bai bar kwallo ya shiga ragarsa ba a wasa tara daga ciki.

Yayin da Madrid ta ci kwallo 27 a lokacin, Karim Benzema ne ya ci bakwai shi kuwa kyaftin Sergio Ramos yana da bakwai.

Real Madrid za ta kara da Cadiz ranar 17 ga watan Oktoba a gida a wasa na shida da za ta fafata a gasar La Liga ta shekarar nan, kuma Real Madrid tana ta daya a kan teburin bana.

Jerin wasannin da ba a yi nasara a kan Real ba a La Liga a 2019-20:

  • Real Betis2 – 1Real Madrid

Ranar 21 ga watan Yunin 2020

Ranar 24 ga watan Yunin 2020

Ranar 28 ga watan Yunin 2020

  • Espanyol 0 – 1Real Madrid

Ranar 2 ga watan Yulin 2020

Ranar 5 ga watan Yulin 2020

  • Ath Bilbao0 – 1Real Madrid

Ranar 10 ga watan Yulin 2020

Ranar 13 ga watan Yulin 2020

Ranar 15 ga watan Yulin 2020

  • Real Madrid2 – 1Villarreal

Ranar 19 ga watan Yulin 2020

Ranar 20 ga watan Satumbar 2020

Ranar 26 ga watan Satumbar 2020

  • Real Betis2 – 3Real Madrid

Ranar 30 ga watan Satumbar 2020

  • Real Madrid1 – 0Valladolid

Ranar 4 ga watan Oktoban 2020

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...