Real Madrid ta fi kowacce kungiyar kwallon kafa arziki a duniya

0

Photo credit: Getty Images

Real Madrid ta zama na daya a jerin kungiyoyi kwallon kafa 20 da suka fi arziki a duniya kwallon kafa bayan ta samu kudin shiga da ya kai fam miliyan 674.6.

Hakan ne ya sa United ta koma ta uku, bayan da Barcelona ta koma ta biyu a karon farko da kungiyoyin Spaniya biyu suka haye teburin a jere tun 2014/15 in ji Deloitte.

An samu kungiyoyin da ke buga gasar Premier shida a karon farko da suke cikin jerin goman farko a jadawalin kamfanin akantoci da ke fitar da kididdigar samun kudi wato Deloitte.

A nazarin da kamfanin ya yi kan samun kudaden shiga a kakar 2017/18, ya fadi yadda kungiyoyin 20 suka sami karin kudin shiga da ya kai kaso 6 cikin dari wato fam biliyan 7.4

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here