Real Madrid na son dauko Aubameyang, Xavi na shirin zama koci

Aubameyang

—BBC Hausa

Real Madrid na son dauko dan wasan Arsenal mai shekara 30 dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang – amma sai idan basu yi nasarar sayo dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund ko takwaransa mai 27 dan kasar Senegal Sadio Mane daga Liverpool ba. (Express)

Kazalika Real na son dauko dan kasar Brazil mai shekara 21 Igor Gomes, wanda za a sayar a kan £45m daga Sao Paolo.(AS – in Spanish)

Newcastle United na sha’awar dauko ‘yan wasan tsakiya na Burnley Robbie Brady da Jeff Hendrick, dukkansu masu shekara 28, idan aka fara musayar ‘yan kwallo. Kwantaragin ‘yan wasan na kasar Jamhuriyar Ireland za ta kare a Turf Moor a bazara. (Newcastle Chronicle)

Dan wasan Arsenal Henrikh Mkhitaryan yana fatan zama dan wasan dindindin daga na aron da yake a Roma a bazara. Arsenal za ta sallama dan kasar ta Armenia mai shekara 31 a kan £18m, amma Roma na son biyan £10m. (Mail)

Dan wasan Barcelona da Spain Xavi ya ce a shirye yake ya zama kocin kungiyar ta La Liga sai dai ya ce ba zai bari a rika samun rashin jituwa tsakanin ma’aikata da ‘yan wasan kungiyar ba. (La Vanguardia – in Spanish

Golan Aston Villa mai shekara 33 dan kasar Ingila Tom Heaton yana so ya zama koci idan ya kammala sana’ar buga tamaula kuma yana sa ran komawa Burnley. (Independent)

Everton na ci gaba da fatan ganin an ba su izinin tsara taswirar sabon filin wasan da suke son ginawa a bazara, duk da annobar da ake fama da ita ta coronavirus pandemic. (Liverpool Echo)

Related Articles