
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Toni Kroos yana da kwantiragin zama a Real Madrid har zuwa ranar 30 ga watan Yuni na 2023
Mai yuwuwa Real Madrid ta ba wa Manchester United dan wasanta na tsakiya Toni Kroos, mai shekara 29, hadi da kudi domin karbar Paul Pogba, mai shekara 26, in ji jaridar Sun.
Haka ita ma Juventus ta ce za ta ba wa United, dan wasan tsakiya dan Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 24, kari da kudi domin dawo da tsohon dan wasan nata, Pogba, kamar yadda Sun din ta labarto.
Arsenal ta shiga layin masu neman dan wasan baya na Norwich, dan Ingila Max Aarons amma kuma Tottenham ce ga alama za ta samu dan wasan mai shekara 19, (Daily Mail).
Kazalika Arsenal din na son sayen dan wasan baya na Bayern Munich da Jamus Jerome Boateng, mai shekara 31. (Sky Sports).
Hakkin mallakar hoto
AFP
Paul Pogba ya sha nuna sha’awarsa ta tafiya Real Madrid
Arsenal ta karkata wajen Boateng ne saboda tana ganin za a fi ta zuba kudi wajen sayen dan wasan bayan RB Leipzig, na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21. (Evening Standard).
Kociyan Everton Carlo Ancelotti ya bayyana cewa Liverpool ta gana da shi domin bas hi aikin kociyanta bayan korar Brendan Rodgers a watan Oktoba na 2015, amma Jurgen Klopp ya doke shi. (Telegraph)
Dan wasan tsakiya na Tottenham, kuma dan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, yana dab da kammala yarjejeniyar tafiya Inter Milan, kamar yadda Ekstra Bladet, ta labarto.
Borussia Dortmund ba za ta sayar da dan wasan gefe na Ingila ba, Jadon Sancho, mai shekara 19, ga Chelsea, sai akalla zuwa karshen kakar nan, kuma dole ne sai Chelsean ta jira daukar shi ma dan gaban RB Leipzig, na Jamus Timo Werner, mai shekara 23, in ji Goal.com