Rasha ta tura dakaru gabashin Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya aike da dakarun soji zuwa yankunan ƴan a-ware na Donetsk and Luhansk da suke a gabashin Ukraine saboda “tabbatar da zaman lafiya.”

Wannan yana zuwa ne jim kadan bayan Shugaba Putin din ya ayyana wadannan yankunan a matsayin masu ƴancin kansu.

Tun a shekarar 2014 yankunan ƴan a-waren suke samun goyon bayan Rasha.

Sai dai ƙasashen Yamma, ciki har da Amurka da Birtaniya, sun nuna rashin amincewarsu ga wannan lamari.

Masu sharhi sun nuna fargabarsu game da abin da ka iya haddasa yaƙi.

Yankunan dai sun jima suna fafutukar kafa kasa mai zaman kanta.

More from this stream

Recomended