Rasha ta nuna damuwa game da asarar rayukan fararen hula a sakamakon sabbin hare-haren da Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren da aka kai ranar Talata sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 326, lamarin da ya kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kwashe kusan watanni biyu ana yi tsakanin Isra’ila da Hamas.
Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana cewa kasar Rasha na matukar damuwa da wannan sabon rikici, wanda ke kara tabarbarewar lamarin a Gaza.
“Babu shakka, wannan wani sabon salo ne na tabarbarewar yanayi a Gaza, wanda ke kara dagula al’amura.
“Abin da ke kara damunmu shi ne rahotannin da ke nuna yawan mutanen da suka rasa rayukansu, wadanda galibinsu fararen hula ne.
“Muna ci gaba da bibiyar al’amarin sosai kuma muna fatan za a koma kan hanyar zaman lafiya,” in ji Peskov.
Rasha Ta Nuna Takaici Kan Asarar Rayukan Fararen Hula a Sabbin Hare-haren Isra’ila Kan Gaza
