Ranar ma’aikata: Gwamnati ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

An ayyana ranar Litinin 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata ta bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.

Aregbesola, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore, a ranar Juma’a, ya yabawa ma’aikatan Najeriya bisa kwazonsu da sadaukarwarsu.

Ya kara da cewa kokarin da ma’aikata ke yi shi ne ke da alhakin daukakar kasar da kuma mutunta Najeriya a yanzu a cikin kasashen duniya.

“Akwai mutunci a cikin aiki; dole ne mu himmatu da jajircewa kan aikin da muke yi domin yana da muhimmanci ga gina kasa,” inji shi.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe ɗan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa Haɗin Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...