Ranar Lahadi za mu yi Idi a Najeriya, inji Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya ce sai ranar Lahadi za a yi Sallar Idi a Najeriya sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a kasar.

A wata sanarwa da ta fito daga fadarsa, ta ce “fadar mai alfarma da kuma kwamitin ganin wata na kasa ba su samu labarin ganin watan Shawwal na shekarar 1441 ba daga ko’ina a fadin kasar, ranar Juma’a.

Saboda haka ranar Asabar za ta zama rana ta 30 ga watan Azumin Ramadan.”

Hakan ne ya sa Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Majalisar Koli ta Addinin Musulunci suka yanke cewa ranar Lahadi 24 ga watan Mayu wadda ta yi daidai da 1 ga Shawwal 1441 ce ranar Idi a Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da kasar Saudiyya ta ce ba ta ga jaririn watan Shawwal ba a saboda haka za a yi Sallah ne ranar Lahadi.

Ita kuwa makwabciyar Najeriya, Jmahuriyar Nijar ta sanar da ganin watan na Shawwal inda za a yi Idi a ranar Asabar.

Ba wannan ne karon farko da ake samun babban ba tsakanin kasashen duniya dangane da ganin wata na fara Azumin Ramadan da kuma karkare shi.

Hakkin mallakar hoto
Sultanate

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...