Ra’ayin ‘yan APC ya bambanta kan ɓangaren da zai karɓi mulkin Najeriya

A yayin da jam`iyyun siyasa a Najeriya ke duba yankin da za su bai wa takarar shugabancin ƙasar, tuni wasu daga yankin arewa suka fara muhawara a kan wanda ya fi cancantar kujerar.

Wasu dai na ganin cewa yankin arewa da ke fama da matsaloli sakamakon taɓarɓarewar tsaro, ba shi da zaɓi illa ya kankame kujerar shugaban kasa.

Amma wasu kuma na cewa lokaci ya yi da ya kamata a nuna adalci ta hanyar danka wa yankin kudu mulki, tun da arewa ta yi.

Masu ra’ayin cewa bai kamata mulkin Najeriya ya fita daga hannun ɗan arewacin ƙasar ba, suna kafa hujja ne da cewa mai daki ya fi kowa sanin inda ke masa yoyo.

Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham wanda ya kasance jigo a jam’iyyar APC na cewa sanin matsala da halin da arewa ke ciki na cikin dalilin da ya kamata a ce mulkin ya ci gaba da zama a hannun ɗan arewa.

Buba Kwacham ya ce, babu wanda zai tunkari matsalolin da yankin ke fama da su, kamar satar mutane da rikicin Boko Haram, da masifar talauci da koma-baya ta fannin ilimi da sauran matsaloli dangoginsu sai ɗan cikin gida, saboda ƴan magana kan ce wasan da kaka ta jure, uwa ba ta jure ba.

Ba wai ina magana ne akan lallai sai ɗan jam’iyyar APC ne zai yi shugabancin ba, ko ma waye ya kasance ya fito daga arewa,” in ji Buba Kwacham.

Amma masu ra’ayin cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya a shekara ta 2023 kuwa, na cewa rayuwa ‘yar ba-ni-in-ba-ka ce, tun da kudu ta yi halalci, arewa ta ci wa’adin mulki biyu, to ya kamata ita arewa ta sakar wa yankin kudancin Najeriyar.

Dakta Dahiru Maishanu, shi ma jigo ne a jam`iyyar APC, ya ce lokaci ya yi da za’a nunawa kudancin Najeriyar.

”A arewa shugaba Muhammad Buhari ya yi sau biyu, ƙasashen yarbawa shugaba Obasanjo ya yi sau biyu, Najeriya dai ta kowa ce, Najeriya ta kowa ce a wannan lokaci ya kamata a miƙawa kudu maso gabas ko kudu maso kudu, tun da kudu maso yamma ta yi nata.

Wannan shi ne adalci, batun da ake yi na cewa idan Mulki ya fita daga arewa za a samu matsala, yanzu ba ɗan arewar ne ba? Abin da ake bukata, shi ne shugaba nagari, mai adalci da zai shawo kan matsalolin da ake ciki, ya ci gaba da ayyukan da shugaba Muhammadu Buhari ya fara yi,” in ji Maishanu.

Sharhi

A Najeriyar dai kallo ya koma kan jam’iyyun siyasa, wajen ganin yadda za su ɓullo wa maganar takara, tun da a halin da ake ciki, hatta manyan jam’iyyun likimo suke yi ba a san gabansu ba.

Tuni dai gwamnonin jihohin kudancin ƙasar suka haɗe kansu suna cewa lallai sai shugabancin Najeriyar ya koma yankinsu.

Yayin da wasu manyan ‘yan siyasa daga arewacin ƙasar su ma suka manta da bambancin jam’iyya suka ce ba lallai ba a tilas a cikin harka irin ta dimokuradiyya, tun da zaɓe masu yawa suke da rinjaye, sai a bari wanda ya biye allonsa sai ya wanke.

More News

2023: 7 APC aspirants battling for Oyo central senatorial district ticket

No fewer than seven aspirants on the platform of the All Progressives Congress (APC), have indicated interest to represent Oyo Central senatorial district in...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...