
Hakkin mallakar hoto
Tottenham Hotspur FC
Tottenham ta yi wa Burnley ruwan kwallaye har biyar a wasan Premier mako na 16 a filin wasa na Tottenham Hotspur.
Tawagar Mourinho ta samu nasara karo na hudu kenan a dukkanin gasa tun bayan da ya karbi aikin horar da ita, amma a ranar Laraba ne Man United ta katse masa hanzarin cin wasa biyar a jere, inda aka cinye su 2-1 a Old Trafford.
Zakakurin dan wasa Harry Kane ne ya ci biyu tun a minti na hudu da kuma 54, sai Lucas Moura da ya ci a minti na tara.
- Everton ta farfado, ta ragargaji Chelsea
Son Hueng-Min ya zira tasa kwallon ne mai kayatarwa a minti na 32 bayan ya jawo ta tun daga yadi na 20 na gidansu har zuwa yadi na 18 din Burnley kuma ya gara ta ta saman mai tsaron raga Nick Pope, babu abin da ‘yan bayan suka iya yi.
Yanzu haka Son ne dan wasan da ya fi jefa kwallo a raga a sabon filin wasa na Tottenham Hotspur sama da saura, inda ya ci tara, ya bayar aka ci shida a cikin wasa 15 da ya buga.
Ba a tashi daga wasan ba sai da Mousa Sissoko ya kara ta biyar a minti na 74, abin da ya sa Spurs din ta matsa zuwa mataki na 5 kafin Man United da Wolves su buga wasanninsu.
Ranar Laraba Tottenham za ta ziyarci Bayern Munich a gasar Zakarun Turai ta Champions League.