Premier League: Man United ta sake barar da damarta | BBC Sport

Rashford da Solskjaer

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Canjaras shida United ta yi a kakar bana

Manchester United ta kara yin canjaras da Aston Villa 2-2, wanda shi ne na shida cikin wasa 14 da ta buga a bana.

Aston Villa ce ta rike kwallon sosai a minti 45 na farko, kuma a minti na 11 ne Jack Grealish ya jefa kwallon farko.

  • Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

United ta samu damar farke kwallon ne a minti na 42 ta hannun mai tsaron ragar Aston Vill, wanda ya ci gidansu bayan da Rashford ya tunkuyi kwallon da kansa ta dawo ta daki bayan mai tsaron ragar.

Bayan dawowa zagaye na biyu ne kuma Man United ta ci gaba da jan ragamar wasan yayin da Aston Villa ta makale a baya, a daidai minti na 64 ne Victor Lindelof ya kara saka kwallo ta biyu.

Sai dai cikin abin da bai kai minti uku ba Tyrone Mings ya farke kwallon, inda wasa ya zama 2-2, kuma haka aka tashi.

Da United ta ci wannan wasan da ta hada maki 20 kuma ta koma matsayi na biyar a teburin Premier.

Manchester za ta karbi bakuncin Tottenham sannan kuma ta je Etihad a ranar 7 ga watan Disamba.

Related Articles