Premier League: Arsenal ta ragargaji Fulham a wasan farko

Willian da Aubameyang

Bayanan hoto,
Willian ne ya bayar aka ci duka ƙwallo uku a wasan na yau

Baƙin fuska a tawagar Arsenal Gabriel da Willian sun taka rawar gani yayin da ta casa Fulham har gida a wasan farko na kakar Premier ta 2020-21.

Da hannun tsohon ɗan wasan na Chelsea a duka ƙwallo uku da Arsenal ta zira a ragar masu masaukin baƙin.

Shi ma Gabriel wanda aka cefano kan fan miliyan 23 daga Lille, ya ci É—aya a wasansa na farkon.

Arsenal ta murza leda yadda ya kamata, yayin da ‘yan bayan Fulham suka riÆ™a haifar wa kansu da matsaloli.

Alexandre Lacazette ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 8 kafin Gabriel ya ƙara ta biyu minti huɗu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Ana minti na 57 ne kuma Aubameyang ya ci ƙwallo mai matuƙar kyau bayan ya buɗa ɓangren hagu kuma ita ce ƙwallo ta 86 da ya ci wa Arsenal a Premier cikin kakar wasa huɗu.

(BBC Hausa)

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da Æ´an ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an Æ´an sanda da kuma sojoji suna É—aukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar Æ´an sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe É—an Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa HaÉ—in Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...