Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya kirkiri wani shafin gidauniyar neman taimakon kudi da zai taimaka wa asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef wajen taimakon yaran da suka kamu da cutar coronavirus.
Pogba ya kirkiri gidauniyar ne yayin da yake bikin cikarsa shekara 27 da haihuwa a ranar Lahadi, “domin taimakawa wajen yaki da cutar Covid-19”.
Dan wasan kasar Faransan ya ce zai ninka kudin sau biyu in har sun kai fan 27,000 kamar yadda ya nema.
Matsalar wannan annoba ba karama ba ce, musamman ga kasashe matalauta da kuma yaran da ba su da gata, kamar yadda dan wasan ya rubuta.
“Ranar zagayowar haihuwata ce, ina murna da hakan, iyalina da abokaina suna cikin koshin lafiya. Sai dai kuma ba kowa ne ke cikin koshin lafiya ba a yanzu.
“A lokuta irin wadannan ya kamata mu hada hannu wuri daya,” dan wasan ya bayyana.
Za a yi amfani da kudin da za a tara ne wajen sayen safar hannu da takunkumin kare fuska da kuma tabarau na ma’aikatan lafiya.
Ya taba yin irin wannan a ranar cikarsa shekara 26 da haihuwa, inda Pogba ya hada fan 7,360 don samar da tsaftataccen ruwan sha ga kungiyoyin agaji masu wannan aiki.