Sa’o’i kaɗan bayan sanarwar ficewar sa daga jam’iyyar PDP, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi na tattaunawa da shugabannin jam’iyyar NNPP domin komawa jam’iyar.
A ranar Laraba ne Obi wanda na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban kasa dake kan gaba a jam’iyar PDP a zaben 2023 ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar.
Sanarwar sa ta ficewa daga jam’iyyar a hukumance na dauke ne cikin wata takarda da ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu.
Wasu majiyoyi sun fadawa jaridar Politics Digest ce wa tuni aka riga aka saka sunan Obi a matsayin wanda zai takara tare da jagoran jam’iyar NNPP na kasa,Rabiu Musa Kwankwaso.