PDP Ta Yi Allah Wadai Da Matakin Rufe Twitter A Najeriya – AREWA News

VOA Hausa

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta soki matakin da hukumomin kasar suka dauka na rufe kafar sada zumnta ta Twitter.
A ranar Juma’a ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya bada umurnin rufe kafar, kamar yadda mai taimaka masa na musamman Segun Adeyemi ya fitar a wata sanarwa.
“Jam’iyyar PDP na watsi da wannan mataki mara kan gado, na dakatar da kafar sada zumunta ta Twitter.” Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce.
PDP ta kwatanta matakin a matsayin “mulkin kama karya wanda ya dora kasar kan turbar shugabanci irin na danniya.”
Sanawar har ila yau ta ce, dakatar da kafar ta Twitter, yunkuri ne na tankwasa ‘yan Najeriya musamman matasa, don kada su binciki ayyukan gwamnati, tana mai cewa, matakin tamkar take hakkin bil adama ne.
“Jam’iyyarmu ta kadu da matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka wanda ya yi kama da mataki da za a dauka a zamanin da, saboda kawai kamfanin sada zumuntar ya bi ka’idojin kasa da kasa, wajen hana gwamnatin Buhari yin amfani da Twitter don nuna kiyayya ga ‘yan Najeriya.”
Gwamnati ta ce ta dauki matakin ne, saboda amfani “ana yawan amfani da shafin wajen gudanar da wasu ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya.”
Sai dai jama’a da dama na ganin matakin, bai rasa nasaba da goge wani sakon Buhari da kamfanin na Twitter ya yi a ranar Laraba, saboda a cewar kamfanin ya saba ka’idar shafin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...