
Asalin hoton, PDP
Kwamitin amintattu na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP, ya kammala wani zama da ya yi ba tare da cimma matsaya ba a kan murabus din da wadansu mataimaka ga ƴan kwamitin gudanarwar jam’iyyar su bakawai suka yi.
A taron da kwamitin ya gudanar a ranar Alhamis ya ce zai sake wani zama inda yake sa ran samun mafita.
Jam’iyyar PDP na fama da rikicin gida, har wasu na kira ga shugaban jam’iyyar na ƙasa Uche Secondus ya sauka daga muƙaminsa.
Bayan shafe fiye da sa’a uku suna tattaunawar sirri, haka ƴan kwamitin suka tashi ba tare da yanke wata shawara a kan waɗansu manyan rigingimun cikin gida da suke addabar jam’iyyar ba.
Batun masu sauya sheƙa daga PDP zuwa wata jam’iyyar, da na wasu mataimaka ga ƴan kwamitin gudanarwa su bakwai da suka fusata suka yi murabus daga muƙamansu na daga cikin manyan batutuwan da aka gaza cimma matsayar a kansu.
Masu murabus ɗin na zargin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Mista Secondus da rashin kamanta gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jam’iyyar, amma ya musanta.
Ko da yake, wasu ƴan jam’iyyar na zargin cewa masu sauka daga muƙaman nasu da zama karnukan farautar wasu ƙusoshin a PDP, waɗanda ke amfani da su wajen ganin sun kai Mista Secondus ƙasa.
Wasu ƴan kwamitin dai na da ra’ayin cewa ya kamata a bi tanadin da kundin mulkin jam’iyya ya yi na hanyoyin sasanta rikici, ta yadda za a yi sulhu baki-alaikum, da ya haɗa da rarrashi ko ban-baki, idan kuma ta ƙiya… sai a kai ga matakan ladabtarwa.
Amma bayan zaman, shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar PDPn, Sanata Walid Jibril ya ce ba a kai ga cim ma maslaha ba.
“Muna nan za mu ci gaba da magana, ba mu gama meeting ɗin ba. Ba a cimma matsaya ba ne kawai.
“Maganar fitcewar mutane kuwa kan faru ga kowace jam’iyya. Don haka abin da ya kamata a yi shi ne a zauna a yi magana.
“A gaya mana dalilin tafiyar ba wai a dinga fita hakan nan ba dalili ba,” a cewar Sanata Walid.
Burin tsige Mista Secondus
Asalin hoton, PDP
A baya-bayan nan ma gwamnonin PDP sun yi ƙorafi kan yadda APC ta mayar da fadar shugaban Najeriya wajen karɓar waɗanda suka sauya sheƙa
Bayan masu murabus daga PDP, akwai wasu da ba su ɓoye maitarsu ba, ta rashin goyon bayan cewa Mista Secondus ya ci gaba da jagorantar jam’iyyar, musamman irin su gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda a wani lokaci har sukan yi sa-in-sa da juna.
Sannan akwai masu ra’ayin ya kamata a bar Secondus din ya kammala ragowar wata uku ta wa’adin mulkinsa, suna cewa bai kamata a tunkari babban zaben 2023 da rikicin shugabanci ba.
Yayin da wasu ke so a sabunta masa wa’adi, wasu kuma cewa suke lallai a tilasta masa yin murabus, saboda zamansa a kan karagar na da haɗari.
Ibrahim Isa na BBC Hausa ya tuntuɓi Senata Walid Jibril ko da wani tartibin matakin da suka dauka a kan wannan lamarin?
“Mu ba za mu ce wa wani ya sauka ba a yanzu, ba mu kai lokacin ba tukun. Idan muka fara maganar wani ya sauka a yanzu ba mu yi daidai ba.
“Muna da lokaci da za mu yi wadannan abubuwan tukun ba tare da mun samu matsala ba.
“Amma an samu ci gaba, ko don halartar da Gwamna Wike ya yi,” ya ƙara da cewa.
Jam’iyyar PDPn dai tana ƙoƙarin farfaɗowa ne daga kaɗuwar da ta yi sakamakon rashin wasu gwamnoni uku da ta yi, da wasu manyan ƴaƴanta da jam’iyya mai mulki ke mata ɗauki ɗai-ɗai.
Ana haka kuma sai ga wannan guguwar masu murabus ta kaɗa, har ana maganar raba shugaban jam’iyyar da rawaninsa.
A gefe guda kuma ga wasu jihohi tara da ba su samu yin tarukan jam’iyyar ba amma ƴan kwamitin amintattun sun ce za su sake zama.
Sun kuma ce suna da yaƙinin cewa nan da makon gobe za su daidaita kawunan ƴaƴan jam’iyyar.