PDP ta gargadi Ganduje da kada ya tatsi masu makarantu kudade kan lasisi

Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi kira ga gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kada ya sake ya yi amfani da batun soke rijistar makarantu masu zaman kansu wajen tatsar kudade daga masu makarantun da sunan sake tsarin makarantun.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Shehu Wada Sagagi, wadda a ciki take nuna alhini bisa kisan yarinyar nan ‘yar shekara biyar Hanifa wadda shugaban makatantarsu ya sace tare da kashe ta, jam’iyyar ta kuma yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka yi saurin ganowa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kotu.

A kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke lasisin gudanarwa na dukkanin makarantu masu zaman kansu a jihar ne sakamakon abin da ya faru a kan yarinyar, jam’iyyar hamayyar ta ce duk da cewa abu ne da yake da kyau sake tsrain makarantun, to amma ta yi gargadi ga gwamnatin da kada ta yi amfani da wannan dama wajen tsatsar kudade daga masu makarantun.

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...