PDP ta bukaci a gudanar da sahihin zabe a jihar Edo – AREWA News

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP sun bukaci shugaban kasa, Muhammad Buhari da kuma hukumar zabe ta INEC da su tabbatar da anyi zabe na gaskiya mai cike da adalci a jihar Edo, ranar 19 ga watan Nuwamba.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a jawabin bayan taro da suka fitar biyo bayan taronsu da suka gudanar ta kafar Intanet.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Sokoto,Aminu Waziri Tambuwal ya hori jami’an tsaro, hukumar zabe dama sauran masu ruwa da tsaki da su gudanar da aikinsu ba tare da nuna son rai ba.

Kungiyar ta kuma shawarci magoya bayan jam’iyar da su kasance masu sanya idanu sosai dan ganin cewa an kirga kowace kuri’a da aka kadawa jam’iyar.

More from this stream

Recomended