Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya halarci taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya gudana yau ranar Laraba a fadar Aso Rock dake Abuja.
Osinbajo ya halarci taron ne biyo bayan shafe makwanni da yayi yana jiya sakamakon raunin da ya samu a ƙafarsa.
A kwanakin da suka wuce ne aka yi masa aiki a ƙafarsa a wani asibiti mai zaman kansa dake Lagos.


