Osihmen Zai Buga Wasan Najeriya Da Afrika Ta Kudu

Yanzu dai ta tabbata cewa, Victor Osihmen dan wasan gaba na tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eagle zai buga wasan da kungiyar za ta yi da kasar AfrikaTa Kudu.

A baya dai an bayyana cewa bai zama dole dan wasan ya buga wasan ba saboda yana fama da ciwon ciki inda ya cigaba da samun kulawar likitoci abin da yasa bai bi tawagar kungiyar ba zuwa garin da za a buga wasan.

A yanzu dai likitoci sun tabbatar da cewa ya warke garau kuma zai iya buga wasan.

A ranar Laraba ne kungiyar ta Super Eagle za ta fafata da takwararta ta Bafana Bafana a filin wasa na garin Bouake.

More from this stream

Recomended