Ortom ya shawarci Yahaya Bello da ya miƙa kansa ga EFCC

Tsohom gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bukaci takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello, da ya fito daga maboyarsa, ya amsa kararsa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Bello dai ya dade yana takun saka tsakaninsa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, inda ta bayyana cewa ana nemansa ne bayan da ya kasa gurfana a gaban kotu a babban kotun tarayya da ke Abuja inda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shigar da kara a gaban kotu na tuhumarsa da laifin zamba na N80.2bn.

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta kuma sanya Bello cikin jerin sunayen, inda ta bayar da umarnin a kama shi a duk inda aka same shi.

More from this stream

Recomended