Omicron: Ƴan Najeriya na caccakar Birtaniya kan hana shiga Ingila

Matafiya

Asalin hoton, PA Media

Ƴan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana damuwarsu game da matakin da gwamnatin Birtaniya ta ɗauka na haramta wa ƴan ƙasar da wasu kasashen Afirka shiga ƙasarta, wanda ya fara aiki a ranar Litinin 6 ga Disamban 2021.

Gwamnatin Birtaniyan ta ce ta ɗauki matakin ne don yaƙi da sabon nau’in cutar korona na Omicron da ya ɓulla a kasashe da dama.

Wasu jami’an gwamnatin Najeriya da masu amfani da kafofin sada zumunta da dama na zargin gwamnatin Birtaniya da nuna wariya a kan kasashen Afirka.

Masu tafiya Birtaniya daga jihohi daban-daban ne a ranar Lahadi suka yi cikar kwari a filin sukar jiragen saman a Abuja don su samu wucewa kafin cikar wa’adin, amma kuma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

A shafin Tuwita a Najeriya an ƙaddamar da wani maudu’i #Africa wanda aka yi amfani da shi sau fiye da 220,000.

Me ake cewa a shafukan sada zumunta?

Mutane suna ta caccakar ƙasashen yamma da suka haɗa da Birtaniya da Canada kan matakan da suke ɗauka na hana ƴan Afirka shiga ƙasashen nasu.

Yawanci mutane na tsokaci ne kan matakin da Birtaniyan ta ɗauka a kan Najeriya da kuma yadda wasu ƙasashen na Turai ke nuna ƙyama ga Afirka ta Kudu da cewa daga can sabon nau’in korona na Omicron ya ɓulla.

Sannan ana ta Allah-wadai da wasu zanen barkwanci na jaridun wasu ƙasashen Turan a kan batun.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

@BeverlyNaya ta ce: “Zuciyata kan karye a duk lokacin da na ji ƴan Afirka na nuna irin yadda suke matuƙar buƙatar ƙasashen yamma bayan kuma su ne ma ya kamata su buƙace mu.

“Kafafen yaɗa labarai sun yi matuƙar yi mana illa tare da ɓata tunanin ƴan Afrika da yawa.

“Yi bincikenku da kyau, na roƙe ku! Duniyar nan ba komai ba ce idan babu Afirka.”

@Mochievous ya ce: “Ga duk masu cewa Najeriya na ba da satifiket din riga-kafi na ƙarya shi ya sa aka sa mu a cikin waɗanda aka hana shiga Birtaniya, to karanta wannan da kyau.

“Duk wuraren da na je da aka ce min na yi satifiket ɗin ƙarya a wasu ƙasashen ne da ba Najeriya ko ƙasashen Afirka ba.”

Me gwamnatin Najeriya ta ce?

A nata ɓangaren, gwamnatin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Najeriya saboda nau’in korona na Omicron.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu Lai Mohammed ne ya yi kiran yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, yana mai cewa “babu hikima a matakin”.

Ya ce duk da cewa kwamitin yaƙi da korona na shugaban ƙasa zai ɗauki matakin da ya dace, “ni a matsayina na mai magana da yawun gwamnati ina kallon matakin a matsayin zalunci da horo”.

Ya ƙara da cewa matakin na Birtaniya ba a ɗauke shi ta fuskar kimiyya ba, sannan ya bayyana mamakinsa kan “ta yadda za a ɗauki matakin kan ƙasa (Najeriya) mai al’umma fiye da miliyan 200 kawai saboda tsirarun mutanen da suka kamu da cutar”.

Ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriyar sakamakon haramcin tafiyar da aka saka.

Shi ma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways ya soke dukkanin tikitin shiga Birtaniya daga Najeriya, inda ya nemi fasinjojin su sauya lokaci ko kuma wurin tafiya.

Na shiga tashin hankali kan matakin nan saboda iyalaina na Ingila

Umar Lawal Isyaku Kankia wanda iyalansa ke da zama a Birtaniya, na daya daga cikin wadanda suka daura ɗamarar tafiya, kuma ya bayyana wa BBC halin da daruruwan matafiyan suka shiga sakamakon takunkumin na shiga Birtaniya.

“Abin nan ya jawo mana damuwa ƙwarai da gaske musamman mu da iyalanmu suke zaune a can Birtaniya.

“Ya kamata a ce na tafi ranar Laraba, jibi kenan, amma sai a ranar Asabar din da ta wuce na samu labari da daddare cewa ga abin da ke faruwa.

“Abin ya ɗaga min hankali sosai ga mu da muke zaune a nan Najeriya, iyalina kuma na can.

“Ka ga ni ina da takardar zama ɗan ƙasa, amma inda matsalar take shi ne duk da cewa gwamnatin Birtaniyan ta ce irin mu za su iya tafiya, amma sai an killace mutum na tsawon kwana 10.

“A tsawon kwana goman nan a otel za a ajiye mutum kuma shi zai biya daga aljihunsa kudin kwana da na abinci da sauransu.

“Da na lissafa sai na ga kudin sun kai fam 2,300 kusan fiye da miliyan daya kenan kudin Najeriya. Kamar ka ba da kudinka ne fa a kulle ka.

Ya ƙara da cewa da ya je filin jirgi ran Lahadi da safe sai ya ga mutane jingim masu son tafiya, wasu har daga Legas. Sannan ya ce a yanzu dai da suka maƙale ɗin Allah ne kaɗai Ya san yaushe za su haɗu da iyalansu.

“A wajen na ga wacce ta fashe da kuka, sannan na ga wani dattijo da shi ma na ga yana hawaye. Abin dai duk ba daɗi. Akwai wanda iyalinsa ma yanzu haka ba ta da lafiya a can Birtaniya tana cikin matsanancin yanayi.

“Wannan na nuna cewa wasu wajibi ne tafiyar tasu don dalilansu masu ƙwari ne,” ya ƙara da cewa.

(BBC Hausa)

More News

Mutum ɗaya ya mutu wasu sun jikkata a hatsarin motar tankar gas

Mutum ɗaya ya mutu a yayin da wasu biyu suka jikkata bayan da wata tankar gas tayi bindiga ta kama da wuta a Ita-Oshin...

Ɗan Boko Haram Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji

Wani mamba a ƙungiyar ƴan ta'adda ta Boko Haram ma suna, Sajeh Yaga ya miƙa kansa ga dakarun rundunar Operation Haɗin Kai dake arewa...

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...