Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi kira da a kama Ahmad Gulak, shugaban kwamitin gudanar da zaben fidda gwani yan takarar gwamna a jihar.
Hope Uzodimma da kuma Uche Nwosu sune mutanen da aka bayyana a matsayin wanda suke lashe zaben mai cike da rudani.
Shugabancin jam’iyar APC na kasa ya soke zaɓen da aka gudanar kana ya wargaza kwamitin.
Gulak ya bar jihar a wani yanayi dake cike da sarkakiya abin da ya tilastawa reshen jam’iyar na jihar ya bayyana bacewarsa.
Amma da yake bayyana sakamakon zaben a birnin tarayya Abuja, Gulak ya ce Sanata Hope Uzodimma shine ya samu nasara a zaben da gagarumin rinjaye inda ya a zargi Okorocha da yinkurin yin garkuwa da shi.
Ya ce anyi garkuwa da sauran yan kwamitin su 9 bisa umarnin gwamna Rochas Okorocha zargin da Okorocha ya musalta a cikin sanarwar da Sam Onwuemeodo, ya fitar a madadinsa.