Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ‘yan Najeriya kada su taba cire rai game da makomar kasar duk da wahalhalun tattalin arzikin da ake ciki.
A wata hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Litinin, Obasanjo ya bayyana kansa a matsayin mutum mai cike da fata, yana mai cewa yana da yakinin Najeriya za ta kai inda Allah ya nufa.
“Muna fatan dukkan ‘yan Najeriya su samu sabuwar shekara mai albarka. Kuma ina gaya wa ‘yan Najeriya cewa, duk da wahalhalun da muke fuskanta, kada su taba rasa fata,” in ji tsohon shugaban kasar.
“Ni mutum ne mai cikakken fata game da Najeriya, kuma muna da kasa mai albarka.
“Abin da muke ciki yanzu ba shi ne inda Allah yake so mu kasance ba, amma ina da tabbacin nan ba da jimawa ba za mu kai inda Allah yake so mu kai.
“Allah yana so Najeriya ta zama kasa mai albarkar madara da zuma, ba hamada ko wata kasa da ba ta da amfani ba.