Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu .

Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a Lagos.

Busola Kukuyi mai taimakawa matar shugaban kasar kan kafafen yaɗa labarai ce ta bayyana haka a cikin wani saƙo da ta wallafa mai ɗauke da hoton ziyarar.

“Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Cif  Olusegun Obasanjo da kuma mai ɗakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu bayan ta ƙarbi ɓakuncin tsohon shugaban ƙasar da ya kawo ziyarar gaisuwar Sallah,”Kukoyi ta rubuta a shafin X.

Ziyarar na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da aka ga tsohon shugaban ƙasar sanye da hula mai alamar tambarin tafiyar siyasar Tinubu.

More from this stream

Recomended