NNPP ta kori Sanata Kwankwaso

Kwamitin zartaswa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Kwankwaso, sakamakon kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Ku tuna cewa tun da farko shugabannin jam’iyyar sun dakatar da Mista Kwankwaso a babban taron kasa a ranar 29 ga watan Agusta a Legas.

Majalisar zartarwa ta kasa, NEC, ta NNPP ta kafa kwamitin ladabtarwa tare da umartarta da ta gayyaci Kwankwaso domin ya kare zarge-zargen cin hanci da rashawa na jam’iyya da karkatar da kudaden jam’iyya/kamfen cikin kwanaki biyar.

Kwamitin ta yi gargadin cewa rashin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa zai sa a kori Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada a 2022 (kamar yadda aka gyara).

Sakamakon haka, Abdulsalam Abdulrasaq, mukaddashin sakataren yada labarai na NNPP na kasa, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata a Legas, cewa kwamitin zartarwar ta kori Mista Kwankwaso ba tare da bata lokaci ba saboda ya ki amincewa da gayyatar kwamitin.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...