NNPP ta dakatar da Kwankwaso saboda zargin cin dunduniyar jam’iyya

Kwamitin amintattu na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta dakatar da dan takararta a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa zargin zagon ƙasa wa jam’iyyar.

Kwamitin ya kuma dakatar da kwamitin gudanarwa na kasa, wato National Working Committee, NWC.

Haka kuma ta nada sabon kwamitin shugabanni na kasa karkashin Dokta Agbo Major a matsayin shugaban riko na kasa da Mista Ogini Olaposi a matsayin mukaddashin sakataren kasa.

Rahotanni sun nuna cewa dakatarwar za ta yi aiki ne na tsawon watanni shida.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a karshen taron da aka yi a Legas ranar Talata, sakataren kungiyar, Babayo Muhammed Abdulahi ya zargi Kwankwaso da tarayya da shugaban kasa Bola Tinubu, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) Mista Peter Obi, ba tare da izinin jam’iyya ba.

More from this stream

Recomended