Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari a wata mai zuwa saboda tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi sakamakon cire tallafin man fetur a kasar.
Kakakin kungiyar, Ben Upah, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya kara da cewa sun baiwa gwamnatin tarayya kwanaki bakwai don magance wannan batu.
In ba a manta ba dai Shugaba Bola Tinubu, a yayin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, ya bayyana cire tallafin man fetur.
Ba zato ba tsammani matakin ya kara hauhawar farashin kayayyakin, wanda ya kara wa talakawa wahala.
A cewar Upah, ƙungiyar ta bayar da sanarwar yajin aikin a fadin kasar daga ranar 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
“Eh, za a fara yajin aikin a fadin kasar a ranar 2 ga watan Agusta 2023. Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sanarwar hakan,” in ji Upah.
Hakan dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan kungiyar likitoci ta kasa (NARD) ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a kasar.