Nigeria @60: Najeriya ta yi sauyawar matuĆ™ar ban mamaki a shekara 60 – Jega

Daga Mahmud Jega, mai sharhi kan al’amura a Najeriya

Idan wani daga kasashen Turai, Amurka ko kuma wata duniyar wanda ya taÉ“a ziyartar Najeriya a karon farko a shekara ta 1960, kana aka gayyace shi zuwa bikin cika shekara 60 da samun ‘yancin cin gashin kai na Najeriyar, tabbas ba zai gane inda yake ba.

Ba a yadda aka bar mu a shekaru 60 da suka gabata ba ne, don haka masu sake kawo mana ziyara sai sun sake ɗaura ɗamarar shirin shan matuƙar mamaki.

Yawan al’ummarmu ya sauya fiye da Ć™ima. Daga kimanin miliyan 50 a shekara ta 1960, yanzu mun kai kimanin miliyan 200 muna kuma Ć™ara bunĆ™asa sannu a hankali.

Garuruwa da birane sun ƙara bunƙasa a wuraren da a baya tamkar kufai ne.

A cikin shekara ta 1990, lokacin da hukumar zaɓen kasar INEC a wancan lokacin ta shata mazabu, Gwarinpa da ke babban birnin tarayyar ƙasar wani ɗan ƙaramin ƙauye ne.

Amma kuma a lokacin da hukumar ta INEC ta gudanar da shirin rijistar masu kaÉ—a kuri’a a shekara ta 2011, ta Ć™ara bunĆ™asa zuwa wani rukunin gidaje mafi girma a yankin Afirka ta Yamma.

Baƙo ba zai iya saurin gane wurin ba.

Bayanan hoto,
Yadda gadar Carter a birnin Ikko ta ke a shekarun 1950

Har ya zuwa cikin shekara 1970, an zayyana akasarin jihohin arewacin Najeriya a littatafan nazarin kimiyyar ƙasa a tamkar yankin dazukan kasashen Guinea da Sudan.

Amma kuma wani ziri kadan ne a kusurwar yankin arewa maso gabashin kasar mai nisa ya fada cikin jejin yankin Sahel.

A yau, hukumomin kasashen waje sun yi nazari a kan akasarin yankunan Najeriya a matsayin yankin Sahel kana suka hade mu tare da kasashen da ke kan yankin Sahara.

”Ni kam ba zan yi kuka da komai ba saboda na san cewa a cikin shekarun 1960, mun sha ganin manyan tsuntsaye irin su gauraka, da su aladun daji da sauran namun daji a kan hanya tsakanin garin Jega zuwa Birnin Kebbi. Amma a yanzu in ka yi sa’a da har za ka ci karo da habiyoyi kaÉ—an”.

Najeriya na da yankuna uku ne kacal a cikin shekarun 1960, haÉ—a da larduna 24, da aka rarraba zuwa gundumomi da yankuna.

Tuni muka sauya ta yadda da ƙyar za a gane mu, daga yankuna uku zuwa hudu, sannan jihohi 12, suka sake bunkasa zuwa 19, sai 21, sai 30 har ya zuwa 36, ga kuma ƙarin babban birnin tarayya Abuja.

Najeriya ta fara ne da ƙananan hukumomi 300 a shekarar 1976 amma tuni suka haɓaka zuwa 774.

A cikin shekarar 1960 da kuma farkon shekarar 1970, litattafan nazarin kimiyyar kasa sun koya mana cewa Ibadan ne birni mafi girma a yankin Afirka ta yamma, daga nan sai biranen Lagos da Oyo da Osogbo da kuma Kano.

Tun a wancan lokacin miliyoyin mutane a Ibadan suka ƙaura zuwa birnin Legas.

Hukumar Kididdigar Yawan Al’umma ta shaida wa kotun sauraron ba’asi kan Ć™idayar jama’a a shekara ta 1992 cewa, lokacin binciken farko na kafin shirin Ć™idayar jama’a a shekara ta 1987, kashi 20% na gidajen da ke birnin Ibadan babu kowa ciki.

Kan haka ne birnin Legas ya ƙara bunƙasar da yake gogayya da birnin Alƙahira na ƙasar Masar.

Har ya zuwa shekara ta 1980 akwai wani karamin gari maras tasiri a yankin tsakiyar Najeriya da ake kira Abuja, amma a yau masu ziyartarmu za su ga wani ƙasaitaccen sabon birni ne da sunansa ya fito fili ba zato ba tsammani.

Garuruwa huÉ—u ne kawai suke kiran kansu manyan birane a shekarar 1960.

Bayanan hoto,
Filin jirgin saman Calabar a shekarun 1960

Amma a yau akwai garuruwa 36 da ke kiran kansu manyan biranen jihohinsu, ko wanne kuma na kashe kuÉ—aÉ—e masu yawan gaske wajen gina fadar gwamnatocin nasu, sakatariya.

Majalisar dokoki da sauran gine-gine kamar na manyan kotuna da rukunan gidaje da gidajen kwamishinoni da manyan filayen wasanni.

Ko wanne akwai jami’an Ć´an sanda na gwamna da bakinsa da gidajen saukar baki da dakunan tarurruka da kuma hukumomi da dama.

Tun a shekara ta 1960, hanyoyin Najeriya da gadoji su suka fara bunkasa amma daga bisani suka lalace.

”A shekara ta 1967 lokacin da shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya kirkiro jihohi 12, mahaifina ya cika motarsa Ć™irar Holden da dukkanin iyalansa, ya tuĆ™a daga Illori zuwa garin Jega.

”Duk da cewa ya yi ta tuĆ™i ba dare ba rana, ya dauke mu tsawon kwanaki biyu kafin mu isa; babu ko da zirin kwalta a titin daga Ilorin zuwa Sokoto”.

Hanyoyin Trunk A da gwamnatin tarayya ta gina a shekarar 1970, da hanyoyi da dama na Trunk B da gwamnatocin jihohi suka gina da kuma Trunk C wadanda kananan hukumomi suka gina, sun sauƙaƙa wa hanyoyin sufuri a kasar matuƙa.

Amma a yanzu irin wadannan hanyoyi akasari sun lalace sai ramuka tare da haddasa cunkoson ababen hawa saboda rashin gyara.

Za ka ga galibi alamun da aka saba gani a kan hanyoyin tuni duk sun faÉ—i, kama gadojin da aka gina duk akasari babu kariya.

Duka motocin haya na shekarun 1960 kamar su Comer da Austin da Morris da Bedford da kuma Mercedes 911 sun yi É“atan dabo.

Kana motocin hawa na mutane kamar su Peugeot 403 da 404 da kuma 504 da Moskovich da Lada da Citroen da Datsun da Daihatsu da Mazda da Volvo da Land Rover da Vauxhall da Opel Record da Volkswagen Beetle da suka maye gurbinsu duk babu su.

Bayanan hoto,
Bankin Barclays a birnin Ikko a farkon shekarun 1970

A yanzu akwai ƙasaitattun motoci da masu hannu da shuni ke ta shigowa da su kamar su da kai ka ce an yi su ne don gasar wasan tseren motoci Formula One, suna faman gudu a kan hanyoyi masu cike da ramuka.

Baya ga sauyawar ababen hawa, al’adar tuĆ™in ma a Najeriya ta sauya Ć™warai da gaske.

A karkashin tsohuwar gwamnatin gargajiya, ya kamata ne a ce ko wane keke yana da lasisi, kana ko wane kare yana da alama a wuyansa, haka nan ko wane direba ya san ya yi tuki a kan layi daya na tituna daya a duk lokacin da ya hangi wata mota na tahowa.

Amma a yanzu duk da hukumomin lura da manyan hanoyin da ake da su da dama, direbobi na ci gaba da tuĆ™in ganganci, ba sa bin Ć™a’idar tuĆ™i, galibi za ka ga manyan motoci babu fitilun gaba ballantana na birki.

Daukar dalibai a makarantu ya ƙara bunƙasa daga shekara ta 1976 lokacin da aka kaddamar da shirin bayar da ilmin firamare bai daya kyauta UPE.

Bayan shekaru 44 bai ci gaba da zama bai dayan ba, yayin da milyoyin yara suka daina zuwa makaranta. Ba dole ba ne ; iyaye za su iya tura ‘ya’yansu manyan birane su yi barar abinci.

Amma ba kyauta ba ne; makarantu na karÉ“ar kudade a É“oye daga dalibai da dama kana dole iyaye su É—inka wa ‘ya’yansu kayan sakawa na makaranta, kana su ba su na abinci da na abin hawa.

Ba lallai ya zama samun ilmin ba, tun da dalibai da dama kan gama makarantar ba tare da sun iya rubuta sunayensu ba.

Akwai asibitocin gwamnati da dama a yanzu da ake kira janaral ko na ƙwararru ko na koyarwa da na kuma tarayya.

Asibitocin janar galibi ba su da isassun likitoci, magunguna ko kuwa gadajen kwanciyar marasa lafiya.

Shi kuwa asibitin kwararrun da wuya ka samu ƙwararrun likitocin ko kuma ma in da akwai za ka ga babu kayan aiki da zai sa su iya gano cuta.

Koyarwar da ake yi a asibitocin koyarwa da na tarayya ba abin a zo-a-gani ba ne.

Amma a duk lokacin da ma’aikatan jinya ba su tafi yajin aiki ba, suna ceton rayukan ‘yan Najeriya da dama, yayin da masu hannu da shuni ke tafiya asibitocin kasashen waje saboda cutar zazzabin cizon sauro.

Shekaru sittin da suka gabata jaridu da rediyo su ne suka fi mamaye labarai a Najeriya. Editoci kan dauki tsawon lokaci wajen wallafa labaran abubuwan da suka faru a mako guda amma duk da haka masu karantawa sukan karanta cikin jin dadi.

Bunƙasa cikin sauri da gidajen talabijin suka yi a shekarun 1970 sun kuma sauya wannan.

Bayanan hoto,
Gaban ginin London and Kano Trading Company da ke birnin Ikko a 1960

Kana zuwa kamfanin daiilancin labaran Najeriya NAN a shekara ta 1978 ya ƙara kawo ci gaba a wannan fanni, yayin da kuma zuwan internet da shafukan sada zumunta sun mayar da yada labarai cikin sauki da kuma sauri, inda yanzu reshe ya juye da mujiya, inda editoci kan samun labarai daga masu karanta labaran ba kamar a da ba.

A baya rubuta wasika wani salo ne a Najeriya, inda dalibai kan dauki lokaci tare da duba litafin Roget’s Thesaurus kafin su rubuta wasikun soyayya.

Su kan samu tambarin da ake mannawa kana su kai ofishin aikewa da sakon wasiku wanda a ko da yaushe za ka samu a tsakiyar birane.

Kana sai sun jira har na tsawon makonni kafin su samu sakon amsar wasiƙun.

”Wata rana an taba samun damuwa a makarantarmu, lokacin da muka ji cewa motar daukar wasiku ta yi hadari; kowa ya ce yana tsammanin sakon wasika”.

Sakon kar-ta-kwana na ‘telegrams’ sun fi sauri a wancan lokaci amma sai dai akwai tsada, za ka biya kudi kan ko wane harafi ne.

Tun da bayan wannan lokaci zuwan su rediyo da talabijin da injinan sakon fax, wayoyin salula da sakon kar-ta-kwana, da email da messenger da Facebook da WhatsApp da Instagram sun sauya yadda ake rubuta wasikun soyayya fiye da ƙima.

Muddin bakonmu yana tsammnin sako daga gida a yau, me yiwuwa ba a wasiƙa zai gani ba, zai kawai samu saƙonsa daga latsawa daya.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...