
Wani tsagi na jam’iyar Labour Party ya nada Nenadi Usman a matsayin shugabar riko ta jam’iyar.
An zabi Usman ne biyo bayan wani taron shugabannin jam’iyar da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja
Darlington Nwokocha tsohon sanata mai wakiltar mazabar Abia ta tsakiya shi ne wanda aka zaba a matsayin sakataren riko na jam’iyar.
Nadin da aka yi wani bangare ne na kokarin da tsagin yake yi na sake samarwa da jam’iyar shugabanni gabanin zaben sabbin shugabannni a wurin babban taron jam’iyar na kasa da za ayi.
Ana saka ran sabon shugabancin rikon da aka samar zai jagoranci ayyukan jam’iyar har sai an zabi sababbin shugabannin a wurin babban taron jam’iyar na kasa.
A yayin taron na ranar Juma’a shugabannin jam’iyar sun amince da jadawalin gudanar da zaben shugabannin jam’iyar a matakin mazabu, kananan hukumomi, jihohi da kuma shiyoyi da kuma na kasa baki daya.