NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na naira miliyan 80 a Abuja

Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ce jami’anta dake Abuja sun samu nasarar kwace kilogram 3900 na miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira miliyan 80 a cikin watanni huɗu na karshen wannan shekarar.

Kabir Tsakuwa kwamanda a hukumar shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

Ya ce miyagun kwayoyin da aka kwace sun haɗa da hodar ibilis ganyen tabar wiwi, Metamphetamine, kwaƴar Tramadol, Diezapam da kuma Rophynol.

Ya kara da cewa jumullar mutane 134 aka kama da ake zargi da sha, safara da kuma sayar da miyagun kwaƴoyin.

More from this stream

Recomended